
Shi ne wanda zai suranta abu kuma ya kayatar da shi. Al Musawwir (المصور) The Fashioner of Forms Allah Maɗaukaki shi ne mai kayatar da siffar ababen halitta.Tsawo ko gajarta, kauri ko sirintaka, a tsaye ko a kife, dunƙulalle ko miƙaƙƙe, mai motsi ko sandararre. Shi ne wanda yake ba kowane abin halitta siffarsa. Al Baari (البارئ) The Maker Allah Albari'u mai kagen halitta, wanda bai gani a gurin kowa ba.
Abin da babu shi sai ya samar da shi ba tare da yaga samfu ba a gurin wani.
Al Khaaliq (الخالق) The Creator Allah shi ne mai samar da komai daga babu.
Al Mutakabbir (المتكبر) The Tremendous Allah Maɗaukaki shi ne wanda ya kadaita da girma da ɗaukaka, ba wani girma ban da nasa. Komai mutum zai yi sai in ya dace da abin da yake so, in bai dace ba shi ke nan yayi asara. Amma Shi kuma ba wata Irada da take iya ratsa Shi. Shi ne mai karya ƙashin bayan masu taurin kai. Al Jabbaar (الجبار) The Powerful, the Irresistible Allah shi ne wanda komai dole ne ya ƙasƙanta a gabansa. Al Aziz (العزيز) The Almighty, the Self Sufficient Allah shi ne Buwayayye shi ne mai ƙarfin da babu wanda zai iya tankwara shi, shi ne wanda ya kadaita da ɗaukakarsa. Al Muhaymin (المهيمن) The Guardian, the Preserver Allah shi ne mahalicci mai gani ga duk aikin bayinSa. Duk mai neman goyon baya a wajen Ubangiji to ya rinƙa yawaita karanta Ya Mu'minu! Amintaccen sarki. Al Mu'min (المؤمن) The Guarantor The Guardian ( waliyi, mai kula da, majiɓinci, mutumin dake tsaran lafiyan wani mutum) of Faith ( addini, amana/ amanna, bangaskiya, tauhidi) The Faithful ( amintacce, na Imani) Wanda ya amintar da bayinSa daga dukkanin abin tsoro, babu kwanciyar hankali sai daga Ubangiji, me gasgata kansa da kansa. As Salam (السلام) The Source ( mafari, majiya, asali, tushe, salsala, masomi) of Peace ( zaman lafiya, sulhu, kwanciyar hankali, amana, aminci, salama) and Blessing The Flawless (babu/rashin aibi, marasa aibu) Allah shi ne wanda Zatinsa da aikinSa suke kuɓuta daga dukkan tawaya, shi ne kuma me kuɓatar da bayi daga dukkan wata halaka, shi ne me tabbatar da aminci tsakanin bayinSa. Al Quddus (القدوس) The Most Holy, Pure ( mai tsarki) Allah shi ne mai tsananin tsarkaka daga dukkan tawaya ko duk abin da mabarnata suke danganta masa. Al Malik (الملك) The King, The Sovereign Lord ( mamallakin sarki ubangiji) Allah ne ma'abocin mulki isasshe wanda ba shi da buƙata a cikin halittarsa, kuma mulkin nasa ba ya karewa, kuma shi ne wanda makarfafar komai take ikonSa. Wanda idan bala'i ya sami abin halitta sai ya bashi mafita. Ar Rahim(الرحيم) The Most Merciful Mai jin ƙai, Allah ne mai madauwamiyar Rahama, wanda in ba a roƙe shi ba, sai yayi azaba. Ar Rahman (الرحمن) The All Merciful ( mai jin ƙai) The Compassionate ( mai tausayi, mai juyayi – alhini), The Beneficent (Mai rahama) The Infinitely ( rashin iyaka, mai yawa) Good Allah mai yalwar Rahama ne wacce ta game bayi gaba ɗayansu, Musulmi ko Kafiri, Me biyayya ko me saɓo. The 99 Names of God (Allah) according to the tradition of Islam are: The 99 Names of God (أسماء الله الحسنى), ʾasmāʾu llāhi lḥusnā) also known as The 99 attributes of Allah, according to Islamic tradition, are the names of God revealed by the Creator(God) in the Qur'an.